Advertising

Yadda Teemah Makamashi ta yi walimar naɗa ta Jakadiyar Kwalliya kuma Jakadiyar Zaman Lafiya ta Arewa

Advertising

A sakamakon nada teema sarautu guda biyu da masarautar Gombe ta yi mata a ranar 25 ga Agustan da ya gabata, jarumar Kannywood Hajiya Fatima Isah Muhammed (Teemah Makamashi) ta shirya wani ƙasaitaccen biki domin murna.

Sarautun nata su ne Jakadiyar Zaman Lafiya ta Arewa da kuma Jakadiyar Kwalliya,An gudanar da taron murnar a ranar Juma’a, 6 ga Oktoba, 2023 a wani ɗakin taro da ke Titin Haɗeja a birnin Kano, kuma ya samu halartar ɗimbin jama’a daga sassa daban-daban.

Advertising

A wajen taron, mawaƙa irin su Fati Nijar sun baje kolin waƙoƙin su inda aka ɗauki lokaci mai tsawo ana nishaɗantar da mahalarta,An gudanar da liyafar cin abinci ta musamman, daga nan kuma sai Teemah ta shigo cikin taro ta na rawa ana yi mata liƙi wanda aka riƙa yi har zuwa ƙarshen taron.

Taron ya samu halartar wakilai daga masarautun Kano, Bauchi, Gombe da Katsina, Haka kuma akwai wakilai daga gwamnatin Jihar Kano da kuma ‘yan fim da su ka haɗa da Yakubu Muhammad, Sulaiman Garba, Saratu Giɗaɗo, Mansurah Isah, Aisha A. Musa da sauran su Kamar Yadda Zakuga Hotunan Dinnar

Da Fatan Allah Ya Bada Ikon Rike Sarauta Ameen.

Share to

Check Also

Yadda Aka Sacewa Wani Balance Dinsa A Garin Bauchi State

Advertising Wallahi Wallahi Wallahi yanzu yanzu wannan abun ya faru a cikin garin Bauchi, wannan …