Advertising

Abuna Mamaki Yadda Dattijo Da Be Taba Zuwa Makarantar Ba Ya Kirkiri Na’urar Sadarwa

Advertising

Dattijo dan shekara 70 wanda be taba zuwa makaranta ba, ya kirkiri na’urar sadarwa ta Rediyo, Injin Vespa, jirgi mai saukar angulo, wayar salula, da sauransu.

Idan kaji ana kiran “Nigeria Get Talent” to da wannan bawan Allah ake.

Advertising

Engr Hadi Usman, shine Wanda ya ƙirƙiri gidan Radio mai zaman kanshi tun wajen Shekarar Aluf da Ɗari Tara da Saba’in banda gidan Radio ya ƙirƙiri wayar salula da injin jirgi mai saukar Angulu da mashin vespa da sauran su, (Radio transmitter, Vespa engine helicopter, telephone (handset)).

A baya bayan nan ya ƙirƙiri wani injin bada hasken wutar lantarki Wanda baya Buƙatar amfani da Man fetur domin bada hasken wutar lantarki haka ma ya ƙirƙiri Murhun Girki da yake amfani da Ruwa domin amfani dashi wajen yin girki.

Engr Hadi ya sauka Jami’ar jihar Gobe Inda ya gabatar da wasu fasahohin ƙirƙira da yayi yayin da ake bikin yaye ɗalibai ƴan zangon karatu na, 11th, 12th da 13th a Jami’ar ta Gombe.

Wani abun burgewa shine Injiniya bai taɓa halartar makarantar boko ba, amma dai Mahardacin Al-qur’ani mai tsarki ne tun yana Ɗan Shekaru Goma Sha Biyu 12 a duniya.

Hadi Ɗan asalin jihar Gombe ne daga yankin Jekadafari Allah ya ƙara basira Amin.

✍️ Muhammad Aminu Kabir.

Share to

Check Also

Yadda Aka Sacewa Wani Balance Dinsa A Garin Bauchi State

Advertising Wallahi Wallahi Wallahi yanzu yanzu wannan abun ya faru a cikin garin Bauchi, wannan …